Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a zaɓen Shekarar 2019 Alhaji Garba Sani Danƙani Jikan Hambali, yace jam’iyar APC nada bukatar jajirtattun mutane irin tsohon Gwamnan Jihar Katsina Barrister Ibrahim Shehu Shema.
Haka zalika, Alhaji Hambali ya hori ƴaƴan Jami’iyyar APC a Jahar Katsina dasu tabbatar sun zaɓi shuwagabanni nagari a zaɓen shuwagabannin jami’iyya mai zuwa na ranar Asabar.
Alhaji Garba Dankani Jikan Hambali na magana ne a lokacinda yake karbar kungiyoyin matasa masu sana’oin hannu su 25 da sukayi mubaya’a ga tafiyar Hambaliyya Karamchi.
Jikan Hambali yace Jam’iyar APC a Jihar Katsina nada matukar buƙatar fasihan mutane irin su Barrister Shema da Sanata Yakubu Lado Danmarke gami da Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Majigiri domin samun nasarar Jam’iyar a zabukan gaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar ‘Yan Sandan Neja Sun Cafke Masu Safarar Bindiga Mutum 3 Sun Kwato Harsasai 567
Yace tafiyar shi ta Hambaliyya a shirye take ta hada karfi da karfe, da Barrister Shema da Sanata Yakubu Lado, da Sauran dukkanin wani Mai rajin kawo cigaban Jihar Katsina, domin ganin an gudu tare an tsira tare.
Alhaji Garba Sani Jikan Hambali ya Maganta akan dumbin tsare-tsare da yayi na kawo cigaban jihar Katsina idan Allah ya bashi damar zamo wa Gwamnan Jihar a Babban zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.
Daga nan sai ya nuna Farin ciki akan yadda matasan Suka yanke shawarar mara Mashi baya a siyasance, sai yasha alwashin cewa zai tafi da su domin samun nasara.
Yayi amfani da damar inda ya bukaci ƴaƴan Jam’iyar APC a Jihar Katsina, da su zaɓawa Jam’iyar Shugaba nagari a zaɓen Shugaban Jam’iyar na Jiha dake tafe nan da makonni masu zuwa.
A nasu jawabin, mai magana da yawun Kungiyoyin, sunce sun yanke shawarar bin tafiyar Hambaliyya ne lura da gudummuwarda yake bayarwa ga cigaban matasa, ta hanyar tallafa masu domin su kasance masu dogaro da Kai.
Daga nan sai sukayi Kira ga Sauran Yan siyasa da suyi koyi da Jikan Hambali ta fuskar rashin gudun Jama’a.
Sauran wadanda Suka Maganta sun haɗa da Babban Jami’in Hambaliyya na Jiha Malam Habibu Liman, da Alhaji Kasimu, gami da Samira Musa da Amina Musa da dai sauransu.
Sunyi magana akan kyawawan halaye na Alhaji Garba Sani Danƙani Jikan Hambali, sai suka yi mashi addu’a akan Allah SWT yayi mashi jagoranci a harkokinshi na Siyasa.