Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya bukaci matasan Najeriya da su zabi wadanda ke da suka yi abun azo agani, a yayin babban zaben shekara mai zuwa. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Shugaban majalisar ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) karkashin jagorancin shugabansu Usman Barambu suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke majalisar dokokin kasar nan a babban birnin tarayya Abuja.
Ya shawarci matasan da su nemi shugabannin da ke da tarihin abun azo agani, yana mai cewa a wasu kasashen, mutane su kan gabatar da ayyukansu na baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: AU Ta Sanya Ranar Zaman SulhunTa Gwamnatin Habasha Da Yan tawayen Tigray
Gbajabiamila ya shaida wa daliban da suka kai masa ziyarar “godiya” kan rawar da ya taka wajen warware yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU) ta yi na tsawon watanni takwas, inda ya ce, ba kowa ya ke iya yin hakan ba, amma ya bukace su da su duba tarihin wadanda ke kan gaba a zaben shugaban kasa dake tafe
Ya kuma cigaba da cewa, idan dan takara ba shi da tarihin da zai yi takara kuma yana magana akan wani abu na daban, yana nufin cewa ba shi da kwazon da zai iya yin takara, don haka bai cancanci a kadamasa kuri’a ba.
Sai dai ya bukaci daliban da su yi addu’ar Allah ya do rasu akan tafarkin da ta dace donmin yin zabi nagari.
A WANI LABARIN KUMA: An Saka Ranar Da Za A Gudanar Da Zaben Maye Gurbin Firaministan Burtaniya – Mahukunta
A wani abin da ya ba wa duniya mamaki, Fira ministar Birtaniya Liz Truss, mai shekaru 47, ta yi murabus a ranar Alhamis din nan, bayan wasu batutuwan da suka shafi tattalin arziki da suka dabaibaye kasuwannin hada-hadar kudi na Burtaniya, lamarin da ya kai ga tayar da kayar baya a jam’iyyarta ta Conservative.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu ta rantsar da Truss a matsayin shugabar gwamnatin Burtaniya a ranar 6 ga Satumba, 2022, kuma ta yi murabus bayan kwanaki 45 tana mulki a ranar 20 ga Oktoba