Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi dan takarar da suke so a zabe mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya ce ‘yan kasar nan su yi zabe ba tare da tsoro ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba mu ajiye wa wani yanki shugaban kasa — Dattawan Arewa
Da yake jawabi ga ‘yan Najeriya a wani shiri da aka watsa a fadin Najeriya Buhari ya sha alwashin tabbatar da tsaro a lokacin zabe.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su guji tashe-tashen hankula da ayyukan da ka iya kawo cikas ga harkokin zabe.
A cewar Buhari: “Don haka ina kira ga kowane dan kasa da ya fito ya zabi ‘yan takararsa ba tare da tsoro ba, domin za a samar da tsaro kuma kuri’ar ku za ta yi amfani.
“Duk da haka ina yi muku gargaɗi da ku guji tashe-tashen hankula kuma ku guji ayyukan da za su kawo cikas ga harkokin zaɓe. Ina yi mana fatan Allah Ya sa mu yi babban zabe cikin nasara.”
A wani labari kuma, Sake Fasalin Naira: Ina Son Hana Amfani Da Kudi Ne A Zabe – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince cewa wani bangare na shirinsa na amincewa da sake fasalin kudin Naira shi ne rage amfani da kudi a lokutan siyasa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya bayyana haka ne a safiyar ranar Alhamis yayin wani jawabi da ya yi wa Yan kasar nan.