Akalla masu tada kayar baya 9 su ka mutu sanadiyar rashin jitu wa da ya auku tsakanin bangarorin Yan bindigan daban-daban a jihar Kaduna.
Gwamnatin jihar Kaduna ce ta bayyana hakan jiya Juma’a a wani rahoton leken asiri da jami’an tsaro suka tabbatar da mata da hakan.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, wannan rikici ya auku ne ranar Larabar data gabata, a karamar hukumar Giwa dake a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Yobe ta bukaci a karawa jihohi, da Kananan hukumomi kudade
An ce wani shahrarren dan bindiga mai suna Godon Mota ya dira kauyen Garke tare da Mabiya sa, kuma suka tada yamutsi.
Duk da cewa ba’a tabbatar da takamammen abinda ya haddasa rigimar bar ba tsakanin bangarorin biyu, Amma majiyoyi daban daban na nuna cewa, rikicin na da alaka da rabon kudin fansa.
Kazalika Daya daga cikin kungiyoyin, sun yi zargin cewa, an cucesu wajen rabon wasu makudan kudade, Wanda ake kyautata zaton cewa, kuma hakan ne ya haddasa rikicin.