Duk da irin Makudan kudade da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ke bayarwa a matsayin Kudin fansa, Hakan bai sassauta zuciyar masu garkuwa da mutnen ba inda a hannu guda suka sake mika bukatar da a kai musu buhunhunan Shinka da Kayan girki, kari kan kudin.
Cikin watanni ukku kachal, mutanen kuyukan dake Kananan Hukumomin Kuje da Kwali da Gwagwalada gami da Ƙaramar Hukumar Abaji dake birnin tarayya Abuja sun ga ta kan daga hare-haren masu garkuwa da mutane inda suka yi awun gaba da mutane talatin a ɗan tsakanin lokacin.
To sai dai a sace mutanen da aka yi a yan baya bayan nan a yankin Kiyi da Anguwar Hausawa dukkanin su dake Kananan Hukumomin Kuje da Abaji, baya ga miliyoyin kudi da suka bukata, masu garkuwan sun bukaci iyalan Mutanen da su taho da buhunhunan Shinkafa da taliya da kuma kwallayen Magi.
Rahotanni sun ruwaito cewa tuni iyalan wasu mutane takwas ciki har Faston Cicin RCCG dake Kiyi suka yi wa kan su Kiyamul Laili suka siyo kayayyakin abincin don gudun abinda zai kai ya komo.
Daya daga cikin dan uwan wani da aka yi garkuwa da shi a yankin Kiyi da aka bayyana shi da Joshua, ya bayyana cewa fargabata ta sanya su ala tilas sai da suka Buhun Shinkafa biyu da katon din Indomie kana ya haɗa da garin kuɗi har naira miliyan guda da rabi.
Ya kara da cewa, ba shi kaɗai ba ma akwai iyala da dam da suka bi umarnin masu garkuwan gabannin sakin yan uwan su.Ya ce ko da mutum kunnen uwar Shegu ya ƙi siyan kayan abincin, to za su karɓe kuɗin sannan su ci gaba da rike maka yan uwa har sai kayi wa kan ka Kiyamul Laili.
A hannu guda shi ma wani mai suna Mista Isaac Jonathan da aka yi garkuwa da dan uwan shi, ya ce ala tilas Sai da ya sayi buhun shinkafa biyu da magi da katon-katon na taliya da Kwalayen taba sigari gami da kwalaben barasa gabannin sakin dan uwan nashi da aka sace a kauyen Shenegu dake karamar hukumar Gwagwalada.