Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya ce kamata ya yi a gayyaci tsofin Hafsoshin tsaron kasar nan su yi bayani kan kudin makamai ba wai shi ba
Hafsan Sojin wanda ya yi wannan magana ne a yayin da ya gurfana gaban kwamitin wucin gadin majalisar wakilai dake binciken yadda aka batar da kuɗaɗen makamai duk takaitattun bayanai da majalisar ta bukata ya gabatar mata da shi.
Ya Jaddada bayanin cewa dukkanin Kundin bayanan da ya mika suna dauke da bayani dalla-dallah kan yadda aka yi amfani da kudin makaman inda ya umarci majalisar da ta gayyaci tsofin Hafsoshin Sojin da su gurfana su yi mata karin bayani.
Wani dan majalisa daga Jihar Delta mai suna Ejiro Ogene yayin zaman kwamitin ya hakikance cewa lallai fa bai ga dalilin da zai sa Hafsan Sojin ba za gurfana gaban majalisar ba.
Ya kara da cewa majalisar dokokin kasa ta yan kasa ne kuma duk wani mai rike da mukaman gwamnatin yana aiki ne wa yan kasa, don haka majalisar tana magana ne a madadin yan kasa.
“Lokacin da muka gayyace ka da ka gurfana, to yan ƙasa ne ke gayyatar ka ba mu ba, don haka idan ka yi karya to abubuwa ka iya sauyawa”
“Ni a zato na Hafsan Sojin zai bada hakuri ne, ba wai kuma ya zo yanabayanin kare kan shi ba, saboda tamkar al’umma ce ta zabe ka”