A Yau Talatar ce Majalisar Dattawa ta shiga wani zama na sirri domin daukar matsaya kan kin amincewa da Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya yi na kin sanya hannu kan dokar gyara zabe.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya isa zauren majalisar, inda ya gabatar da addu’o’in bude taro da karfe 10:42 na safe, ya kuma bayyana cewa majalisar za ta shiga wani zama na sirri.
Shugaba Buhari dai ya ki amincewa da kudirin dokar zabe ne, bisa dalilan tsaro, kashe kudi da sauran abubuwan da suka shafi tsarin zaben kasar da kuma jam’iyyun siyasar kasar.
An dai lura da cewa wasu Sanatoci kalilan ne suka kasance a zauren majalisar kafin a fara rufe zaman.
An yi imanin cewa ‘yan majalisar za su tattauna batun kin amincewa da kudirin da kuma daukar matsaya kan kudurin da kuri’u biyu bisa uku.