• Kudurin na da matukar mahimmanci ga harkan banki da kudaden
•Sauran ta kwarorin shi sanatoci sun amince da kudurin.
• Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya to fa nayi albarka cin dangane da mahimmin kudurin.
Sanatan Kaduna ta tsakiya Malam uba sani ya gabatar da Kudirin Dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade ta shekara ta 2004 da aka gabatar a shekara ta 2019, da nufin inganta bangaren ajiya da hada-hadar kudade a Nijeriya,
Tuni shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa kudurin hannu, ya kuma zama doka a tarayyar Nijeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gaskiyar lamari dangane da auren Iyantama da Rashida Mai sa’a
A ranar 13 ga watan Nuwamba na shekara ta 2020, kuma sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, tuni ta hada kafada da sauran kasashen duniya, wadda za ta inganta tsarin karba, da kuma bada Lasisin gudanar da Bankuna.
Sannan dokar za ta samar da sararin fayyace ainin hakkin babban bankin Nijeriya da sauran cibiyon hada-hadar kudade.
Haka kuma, dokar za ta sa ido, a kan kamfanonin kimiyyar sarrafa kudade, da irin hukuncin da zai biyo bayan, duk wata munakisa ko harkallar kudi.
Idan za a iya tuna wa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana, “Dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade ta shekarar 2020, ta kasance abin tarihi, kuma wani ci-gaba a bangaren tafiyar da harkokin kudade a Nijeriya.” Inji Buhari
Comments 1