By Ishaq Dabai
Kungiyar likitocin masu neman kwarewa ta Najeriya NARD a ranar Asabar ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin sa’oi 72 don biyan bashin albashin membobinta a dandalin GIFMIS, da na Asusun Horar da Ma’aikatan Lafiya MRTF.
Ta bayyana cewa yajin aikin da aka fara a ranar 2 ga watan Agusta, 2021, don kawo karshensa, akwai bukatar gwamnati ta biya mafi karancin bukatunta, wanda kuma ya hada da biyan albashin watan Agusta da Satumba da aka hana,na janye karar da aka shigar a gaban kotu, biyan albashi da alawus alawus da ake bin membobinta a cibiyoyin kiwon lafiya na manyan makarantu na jihar, da sauran su.
Shugaban kungiyar NARD, Dakta Dare Ishaya ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a karshen Babban Taron Kungiyar na Shekaru 41 AGM na Taron Kimiyya a Bauchi.
Yace“AGM ya zargi gwamnatin tarayya da kai NARD kotu saboda yajin aikin da ake yi don neman inganta rayuwar membobin mu.” Sun yi tir da mambobin dake cikin mawuyacin hali a dandalin GIFMIS da suke fuskantar saboda jinkirin biyan albashinsu daga watanni uku zuwa takwas.
AGM ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da waɗannan abubuwan cikin gaggawa don manufar dawo da yanayin al’ada ga sashin kiwon lafiya, Biyan Horar da Likitoci masu neman kwarewa a cikin awanni 72, tunda kuɗin da akayi nufin yana samuwa da tabbatar da jerin sunayen don biyan kuɗi an kammala, Biyan basussukan albashin membobin mu akan dandalin GIFMIS a cikin awanni 72 yayin da ake ci gaba da yin ƙaura, Da janye karar da aka shigar damu a gaban kotu don a samu zaman lafiya, Biyan albashin da aka hana a watan Agusta da Satumba.
Yakamata gwamnatin tarayya tayi nasara akan gwamnatocin jihohi daban daban da su gaggauta biyan basussukan albashi da alawus alawus da ake bin membobin mu a cibiyoyin kiwon lafiya na manyan makarantu na jihar kamar yadda aka bayyana a sama.