Kuje kuyi allurar riga-kafi, har yanzu Covid-19 na Yaɗuwa – NPHCDA ga Ƴan Najeriya
Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta shawarci ‘yan Najeriya da su kare kansu daga COVID-19.
Hanifa Hamza, Shugabar Hukumar a Jihar Kwara ne ta bada shawarar a ranar Laraba a wani horon masu ruwa da tsaki a Ilorin.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Wike zai yiwa Tinubu aiki domin yaci Zaɓen Shugaban Ƙasa – Masari
Jami’ar ta buƙaci mutane da su je suyi gwaji, tana mai bayanin cewa kwayar cutar gaskiya ce kuma har yanzu tana yaɗuwa.
Hamza ta kuma tabbatar da cewa akwai isassun alluran rigakafi a fadin kasar nan, kamar yadda NAN ta bayyana.
“Yadda COVID-19 ke yaɗuwa akwai rikitarws. Don Allah kar a huta, zata iya zama kamar mura ko zazzaɓin cizon sauro. ”
Hamza ta yi kira da a yi taka tsantsan, tana mai ƙara da cewa kada mutane su riƙa wanke hannu.
“Ku sha bitamin C, ku ci abinci mai gina jiki akai-akai, yi amfani da hanci da kuma ƙara yawan adadin kuzari,” in ji ta.
Jessica Akinrongbe, Babbar Jami’ar Ba da Agajin Gaggawa ta NCDC ta shawarci mutane ƴan ƙasa da shekaru 60 da su dauki matakan kariya daga cutar.
A WANI LABARIN KUMA: Zaben 2023: Yankin Arewa Maso Yamma Nada Matukar Mahimmanci Ga Nasarar APC – Dattijo