Kuje kuyi Katin Zaɓe indai kuna son ɗorewar Sana’ar ku — Wani Jigo yayi kira ga Ƴan Acaɓa
An yi kira ga membobin kungiyar matuka baburan haya a shiyyar Funtua da su maida hankali wurin mallakar katin jefa kuri’a kafin lokacin rufewa ya yi.
Shugaban kungiyar na shiyyar Funtua Auwal Anda ya yi wannan kiran a lokacin taro da membobin kungiyar a shiyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun Hallaka Manoma a Sokoto, sun ɗora Haraji ga wasu
Ya ce membobin kungiyar nada muhimmiyar rawar da zasu iya takawa wurin zaben sashihan shugabanni da za su ciyar da Najeriya gaba.
Shugaban kungiyar ya kuma yi kira ga wadanda katinsu keda matsala da su je a gyara masu shi cikin lokacin.
Sannan ya bukaci wadanda suka yi rijistar basu amso nasu ba, da suje su amso katinsu ma dindindin.
Haka zalika, shugaban kungiyar na shiyyar ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta aiwatar da sabbin dokokin zaben da aka amince da su yadda ya kamata, don tabbatar da sahihin zabe a fadin Najeriya.