Daga: Abbas Yakubu Yaura
A yayin da ake gudanar da gasar cike gurbin kujerar Alaafin na Oyo, gidan sarautar Agunloye a ranar Alhamis a garin Oyo, sun mika jerin sunayen mutane 48 wadanda ke takarar neman mukami zuwa ga shugaban sarakunan masarautar, wanda aka fi sani da Baba Iyaji, Cif Afonja Mukaila.
A bisa tsarin gargajiya ne ke gadin fitowar sabon Alaafin, Afonja, yayin da shugaban sarakunan Oyo ke da alhakin mika jerin sunayen ‘yan takarar zuwa ga Oyomesi, majalisar gargajiya mafi girma a garin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarki Mafi Dadewa Akan Mulki A Zamfara Mai Kwatarkwashi Ya Rasu Yana Da Shekaru 93 A Duniya
Iyalan sarakuna biyu, wato Alowolodu da Agunloye sune keyin sarakuna a Oyo. Alaafin na Oyo na ƙarshe, Oba Lamidi Adeyemi ya fito daga gidan sarautar Alowolodu.
Da yake zantawa da manema labarai bayan gudanar da wani taro na tantance sunayen sarakunan da suka mika takardar neman zama Alaafin, shugaban (Mogaji) na gidan sarautar Agunloye, Oyo, Yarima Samuel Ademola Adelana, ya ce “Daga jerin sunayen sarakuna 48, mun sallama yau ga Baba Iyaji; muna da tarin ƴan takara tare da zuriyarsu da ƙwarewa don haɓaka zamantakewa da ci gaban tattalin arzikin garin Oyo.
Ya ce: “Makasudin taron na yau shi ne tattaunawa kan wasikun sha’awa da kuma bayanin jerin sunayen sarakunan da suka gabatar mana a cikin gidan sarautar mu, da ke neman kujerar Alaafin Oyo.
“Bayan haduwarmu a nan, za mu kai wasikun zuwa ga Baba Iyaji, shugaban sarakuna a garin Oyo. Mukaminsa shi ne ya karbi wasikun sha’awa daga iyalan sarakuna daga gidan sarautar Agunloye na gaba, wanda ke da hakkin samar da Alaafin din Oyo na gaba.
“A takaice dai, mun bude gasar ne domin dukkan rassa masu mulki a gidan sarautar Agunloye su fito da sarakunan da ke da muradin zama Alaafin Oyo. Taron na yau shine don gudanar da binciken da ya dace akan duk wadanda suka fafata da su kafin mu kai jerin sunayen wadanda suka fafata a gaban Baba Iyaji, Cif Afonja Mukaila, wanda shi kuma zai mika jerin sunayen ga Oyomesi wadanda ke da alhakin zabar Alaafin na gaba.
“Daga gidan mulki na Agure, muna da ‘yan takara biyu; Oke Agbo Gbadegesin, ’yan takara 10; Ilaka Alawuwo, sarakuna tara; Isale Oja, ’yan takara 14 da kuma majalisar mulki ta Ladigbolu sun gabatar da ’yan takara 13. Jimillar ’yan takara 48 ne. Yanzu za mu wuce gidan Baba Iyaji don gabatar masa da jerin sunayen.
“A yau, mun rufe takardar amincewa da duk wani basarake na gidan sarautar Agunloye, dangane da kujerar da Alaafin ya ke da ita.
“Daga sunayen sarakunan da aka mika wa gidan sarautar Agunloye, mun kori mutane uku daga Ife Odan. Mun kore su ne bayan mun gano cewa ba su ne mutanen da suka dace su tsaya takara ko nuna sha’awa ba saboda ba sarakuna maza ba ne. Wasu sarakuna ma Mogajinsu sun hana su.
“Halin da ake ciki yanzu shi ne, a matsayina na uban duk ‘yan takara daga gidan sarautar Agunloye, abin da ya dame mu shi ne addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu mutum nagari a matsayin Alaafin Oyo na gaba, wanda zai bunkasa Oyo da jawo hankalin masu zuba jari zuwa garinmu.
“Lokacin da garin ya shaida ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, za a sami damar yin aiki ga yaranmu da ke yawo saboda rashin aikin yi.”
Comments 1