Shugaban hukumar ta FRSC reshen Jahar Plateau, Gora Wobin, yace hakkin kowane mutum ne dake amfani da hanya ya kula da dokokin kan hanya sannan ya gargadi wanda yake karya ta. Kamar yadd Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Yayi kira da Fasinjojin kada su bari mai tuki ya dunga abunda yaso idan yana kan hanya.
Gora Wobin ya kara jaddada kiransa ga sauran hukumomi da su cigaba da hada karfi da karfe don rage yawan hadura dake wakana a kan hanyoyi.
KARANTA:- Jami’an Custom a Jahar Katsina sun cafke Motoci 13 da buhunan shinkafa 314
Kamar yadda ya bayyana, za su iya taimakawa wajan sanar da mutane dokokin kan hanya, su kuma zama wakilan hukumar inda ba su nan.
Wobin ya nuna sha’awar hadin guiwa da sauran makotan jahohi irinsu Nasarawa, Benue.
Ya janyo hankalin jami’an da su cigaba da kokarin fada da duk masu keta dokar hanya, sannan su kara tsananta yin aiki a kowane lokaci.
Ya bayyana cewa daga cikin dokar, banda yawan lodin mutane, duba da yadda kasar ke fama da cutar Covid-19.
Kamar yadda yace ” an baiwa jami’an mu damar tsananta doka da bincike akan matafiya domin tabbatar da lafiyar su.”
Ya kira ga matuka da su cigaba da tuki cikin lumana tare da bin dokikin hanya a kowanne lokaci.
Shugaban hukumar ya yabawa jami’an rundunar sojojin sama bisa irin taimakawa da sukeyima hukumar, Wobin yace dafatan hakan zai dore.
Haka shima shugaban rundunar sojan sama ya nuna godiyarsa matuka ga hukumar ta FRSC.
Yace Jami’an hukumar ta FRSC na kokari matuka, zaka gansu a duk lokacin da wani hatsari ya auku.
Yayi alkawarin cigaba da hada Kai da hukumar don gudanar da aiki yadda yadda kamata.
Comments 1