Mazauna Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jahar Katsina sun bayyana baƙin cikinsu, na cigaba da hare-haren da ƴan ta’adda suke kaiwa, duk da samame da Sojoji suke kaiwa da wasu matakai da Gwamnatin Jahar ta ɗauka.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da jami’an gwamnati da jami’an tsaro ke cewa matakan da aka ɗauka sun haifar da ɗa mai ido.
Mutane da ƙungiyoyi, musamman a ƙaramar hukumar Faskari na ƙorafin cewa ana yi masu kisan mummuƙe a ƙauyukan su ba tare da wani ya sani ba.
Matakan Tsaro
Ƴan ta’adda sun kasance suna kai hare-hare a jahohin Arewa maso Yamma na kusan shekaru goma, amma lamarin yafi ƙamari a ƴan Shekarun nan da suka gabata. Ta’addanci shine sunan da ake kira wanda ya ƙunshi Garkuwa da mutane, da satar shanu, da satar mutane da yawa, da fashi da makami da sauran su.
Biyo bayan yawaitar kai hare-hare, Gwamnonin Yankin Arewa maso Yamma suka sanya wasu matakai na kawo tsaro a yankin.
A Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari ya kulle wasu manyan hanyoyi guda biyu da suka haɗa da hanyar, Jibia zuwa Gurbin Ɓaure, da kuma Ƙanƙara zuwa Sheme. An kuma shawarci motocin haya da suyi amfani da hanyar Funtua, amma motocin da bana haya ba, zasu iya bin hanyar Ƙanƙara zuwa Sheme.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abubuwan da su ke cikin Sha’irai mata sunfi na harkar fim, cewar Maryam Fantimoti
Gwamnan ya kuma hana cin kasuwannin shanu a ƙananan hukumomi 14, da suka haɗa da Jibia, da Batsari, da Safana, da Ɗanmusa, da Ƙanƙara, da Malumfashi, da Charanchi, da Mai adua, da Ƙafur, da Faskari, da Sabuwa, da Ɓaure, da Dutsin ma, da kuma Kaita.
Gwamnan ya kuma hana ɗaukar dabbobi da icce daga daji. Gwamnan ya kuma hana ɗaukar mutum uku a mashin, da kuma fiye da mutane uku a ɗan sahu da kuma saida man fetur a Jarka, gami da dakatar da kasuwar saida mashina tsofaffi a Charanchi.
Domin hana shigar da man fetur a saman mashina zuwa ga ƴan ta’adda masu kaiwa mutane hari, Gwamnan yace gidajen mai guda biyu aka yarje su sayar da man fetur, kuma baza’a saidawa mutane sama dana dubu 5,000 a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa.
Satittika kaɗan da suka gabata, an datse layukan sadarwa a ƙananan hukumomi 13 da ake ganin anfi kai hari.
Mai baiwa Gwamna Shawara na Musamman akan harkokin tsaro Ibrahim Katsina, ya shaidawa Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya yace an ɗauki matakan domin hana ƴan bindiga sadarwa.
Muna mutuwa a sirrance
ba tare da kowa ya sani ba inji wasu Mazauna a Jahar Katsina
A cikin wata sanarwa da suka tura a ofishin Gwamnan Jaha, Ƙungiyar Haɗin kan cigaban Daudawa tace matakan sun shafi talaka fiye da ƴan ta’adda.
Dayake jawabi akan takardar, Hassan Usman, Shugaban Ƙungiyar yace ƴan ta’adda na kai masu hari a sirrance, inda yace mazauna yankin basu da wasu hanyoyi da zasu sanar da jami’an tsaro akan harin.
“Muna fuskantar taɓarɓarewar tsaro a yanzu fiye da kowane lokaci, sabudda ƴan ta’adda na kai hari da ƙarfin su, sabudda bamu da hanyoyin da zamu sanar da duniya, ko kuma neman jami’an tsaro,” inji Mr Usman.
Duk da ya yabawa Jami’an tsaro dake aiki a yankin, Mr Usman yace suna fuskantar matsalar rashin kira domin neman taimako.
Wuraren da ƴan ta’adda suka kai hari a Katsina
Wasu mutane sun shaidawa PREMIUM TIMES cewa harin da ƴan ta’adda suka kai a Daudawa da Ƴan Nasarawa, dukkanin su a ƙaramar hukumar Faskari, ya sanya dole mutane da dama sun gudu daga al’ummomi da yawa.
A Daudawa, ƴan ta’adda sun kashe mutane 9 da sace wasu da dama, sun ƙone shaguna da dama da sace kayayyakin ciki.
Rana ta biyu a ranar 4 ga watan Oktoba, ƴan ta’adda sun kai hari a Ƴan Nasarawa tare da sace mata da yawa, amma Auwal Hassan Nasarawa yace sunfi kai harin a abinci.
Mai Magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Gambo Isah yace jami’an tsaro sun samu gagarumar nasarar a yaƙi da ƴan ta’adda, biyo bayan kulle layukan sadarwa da akayi a wasu al’ummomi.
Yace kashe-kashe a Daudawa da Al’ummomin Yasore, ƴan ta’adda sun kai shine domin ramuwar gayya.