Kun cika Munafunci da Abun Kunya – PDP ta Caccaki Tinubu, Shettima kan ziyarar Jonathan
Jam’iyyar PDP ta caccaki Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima, kan ziyarar Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
PDP ta bayyana Tinubu da Shettima a matsayin munafukai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nafi Shekaru 10 ina lalata da Ƙananan Yara — Wani Ɗan Shekara 57 da aka kama shi yayi lalata da Ƙaramar Yarinya
Debo Ologunagba, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana yadda Tinubu ya yi caccaka tare da yi wa Gwamnatin Jonathan ƙarya.
A cikin jerin sakonnin Twitter, Ologunagba ya yi gargaɗin cewa hoton Tinubu da Shettima da Jonathan ba zai cece su ba a 2023.
Ya rubuta cewa: “A cikin wani shiri mai cike da matsananciyar sha’awa na zubar da mutunci ga jama’a, tare da bayyana irin nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a fili, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, da Abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima da sauran jiga-jigan APC cikin rashin kunya sun shirya ɗaukar hoto tare da fitaccen Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP.
“Wannan jigo ne mai kishin kasa a Najeriya wanda PDP ta jagoranci gwamnati mai manufa da nasara shugabannin APC suka yi ta muzgunawa, suna zagi, suna ci mashi mutunci, s da kuma bata sunan sa don son kai.
“’Yan Najeriya ba su manta da yadda Asiwaju Tinubu ya yi wa Dakta Jonathan zagon kasa ba, da nuna kiyayya ga Gwamnatinsa, sannan aka ce ya dauki nauyin gudanar da zanga-zangar da aka yi kusa da shi wanda ya hada da karairayi na tattalin arziki, farfaganda, da kididdiga na karya don bata sunan gwamnatin PDP karkashin jagorancin Jonathan.”
A wani labarin kuma: ASUU: Jami’ar Jihar Gombe Ta Janye Yajin Aiki, Ta Bude Rijista ga Malamai
Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a ranar Alhamis ta umurci dukkanin Ma’aikatan Makarantar da su koma bakin aiki cikin gaggawa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta cikin gida mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Satumba mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Dr Abubakar Aliyu Bafeto.