Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi yan ta’addan dake addabar al’umma da kada su kuskura su bari har tura ta kai bango.
Shugaba Buhari na wannan gargadi ne jim kadan bayan wani mummunan hari da ya razana al’umma wanda ya lakume rayukan mutane sama da tamanin a Jihar Zamfara.
Shugaban Kasar ya yi Allah wadai da wannan mummunar aika-aika inda ya ce kada yan ta’addan su yi tsammanin cewa sun gunduri gwamnati, don ana ɗaga musu kafa.
Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun shi kan yada labarai Mallam Garba Shehu, shugaba Buhari ya ce idan har suka bari tura ta kai bango, to lallai za su yi da-na-sanin shiga wannan mummunar aiki.
Da yake umartar jami’an tsaro kan rubanya kokarin su, shugaba Buhari ya ce dole ne su tashi tsaye wajen ganin sun toshe duk wata kafa dake bada yan ta’addan damar musgunawa al’umma.
Yan fashin dajin dai a yan baya bayan nan suna ci gaba da cin karen su babu babbaka a yankin arewa maso yammacin kasarnan, lamarin dake kaiwa ga salwantar rayukan Mutane.