Kwamared Adams Oshiomole yayi kira ga gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad da ya bari a bi doka da oda wajen zaben kakakin majalisar Bauchi -Oshiomole ya ce babu yadda za ayi PDP ta fitar da kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisa a majalisar ta jihar Bauchi
-Oshiomole ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da yan majalisar jihar Bauchi yan jam’iyyar APC.
Shugaban jam’iyyar APC ta kasa kwamared Adams Oshiomole ya ba gwamnan Bauchi Bala Mohammad shawara da ya bi doka da oda wajen tabbatar da cewa jam’iyya mai rinjaye ta fitar da kakakin majalisa, mataimakin kakkaki da sauran shuwagabannin majalisar dokokin jihar Bauchi.
Oshiomole yayi wannan gargadi ne jiya juma’a 21 ga watan Yuni 2019 a lokacin da ya gana da yan majalisar Bauchi na jam’iyyar APC da sauran mukarraban jam’iyyar na jihar ciki hadda tsohon gwamnan jihar Mohammad Abubakar game da matsalar zaben kakakin majalisar jihar.
Ya ce tun da APC ba tayi amfani da karfin mulki ba ta murde ma gwamnan nasararsa, to shima kada yayi amfani da jami’an gwamnati kamar yan sanda, wajen hana ma yan majalisar jihar na jam’iyyar APC yancinsu.
Ya ce an sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan matsalar da ke faruwa, kuma ya umurci babban sifetan yan sanda ya tabbatar da tsaro a majalisar ba wai ya bar yaranshi suna marawa rashin gaskiya baya ba.
Oshiomole ya ce “Babu yadda za ayi PDP ta fitar da kakakin majalisa, mataimakin kakin majalisa, da sauran shuwagabannin majalisa. Idan gwamnan ya nace, to zai janyo ma kansa matsala.
Tun farko, kakakin majalisar na bangaren APC, Kawuwa Shehu Damina, yayi kira ga uwar jam’iyyar da ta taimaka wajen ganin anyi abinda ya dace.
Damina ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kai dauki wajen ganin an kaddamar da majalisar akan ka’ida.