Daga: Abbas Yakubu Yaura
Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya shaida wa ‘ya’yan jam’iyyar cewa Abuja ba karamar karamar hukumar Abia ba ce, kuma kada wani ya zo masa yana kuka bayan zabe.
Adamu, wanda ya bayyana hakan jiya Laraba, a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da kwamitin sulhu na jam’iyyar na Abia mai mutane takwas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Kwamitin Amintattu Na Jam’iyyar Ya Kafa Kwamitin Da Zai Sasanta Wike Da Atiku
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, ya kuma bukaci ‘yayan jam’iyyar da su hada kai tare da hakuri da juna da kuma yin aiki tare domin samun nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Ya ce, “Dole ne mu dauki mataki don mu manta da wasu masu son zuciya mu tsaya tare da wadanda ke son tabbatar da gaskiya, da kuma adalci.
Ba ma son wani ya zo nan bayan zabe ya fara kuka yana dora mana laifin gazawarmu.
“Ba zan saurari hakan ba, lokaci ne da za a hada kai, lokaci ne da za a yi aikin hadin kai, idan muka yi haka, Allah zai kasance tare da mu.
Ya ci gaba da cewa, “Ba za mu sake gudanar da tarukan sulhu ba. Yanzu za mu bar wa shugabannin jam’iyyar na Abia su dauki matakin da ya kamata a jihar.”
“Duk zabukan kasa, ‘yan majalisar wakilai, dattijai, gwamna, watakila zaben shugaban kasa, ba za mu gamsu da kashi 25 na kuri’un da aka kada ba.
“Amma duk da hakan babu damuwa idan za mu yi nasara, dole ne mu yi kokarin lashe kowace jiha,” Adamu ya jaddada.