Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wasu mutane shida da ake zargin suna da hannu a kisan wani yaro dan shekara tara a garin Gusau, kamar yadda jaridar Caliphate Trust ta bayyana.
Rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farautar wadanda suka aikata laifin ne bayan da aka samu labarin cewa an ga yaron tare da daya daga cikinsu a ranar da aka sace shi, Kuma aka kashe shi.
Wadanda ake zargin bayan ‘yan sanda sun yi musu tambayoyi sun bayyana cewa wani mutum ne ya sanya su kashe yaron, tare da ciro sassan jikinsa a unguwar Tudun Wada da ke cikin birnin Gusau.
An ruwaito daya daga cikinsu ya ce tun da farko sun kashe mutane biyu domin yin sihiri. Inda ya Kara da cewa, ya sha fama da mafarkai game da kisan inda yaron da aka kashe ya rika bayyana masa a mafarki yana murmushi.
Daga baya an kama shugaban kungiyar da ke da alhakin kisan gillar, inda ya shaida wa jami’an tsaro cewa shi ne ke da alhakin kashe yaron.
Majiyoyi sun ce wadanda ake zargin sun bayyana sunan mutum daya a cikin ‘yan kasuwar jihar amma ba a iya tantance shi ba.
An gano gawar yaron mai suna Ahmad Aliyu Ijaba a wani ginin Kango a unguwar Barakallahu da ke cikin birnin Gusau a watan Disamba.
Mai ginin ya hango gawar yaron a lokacin da ya je ci gaba da aikin gininsa, nan take ya sanar da ‘yan sanda.
Ahmad ya bace ne jim kadan bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da ke unguwar Gadar Baga a cikin birnin jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma ba zai kara yin magana kan lamarin ba, har sai an kammala bincike.