Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Jihar Kaduna, ta bukaci jami’ar da ta kwace shaidar karatun digiri na gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufa’i.
Kungiyar ta ASUU, tace abinda gwamnan ke yi ya ci karo da koyarwa da kuma kyawawan halaye da Jami’ar ke baiwa duk Wanda ya samu digiri a cikin ta.
Wannan na kunshe ne a cikin takardar abubuwan da aka cimma, bayan taron kungiyar mai dauke da sa hannun shugabanta Haruna M Jibril da sakataranta Hussain A Abdullahi.
Kungiyar tace ta tattauna kan yunkurin gwamna El-Rufa’i na kwace filaye mallakin jami’ar ta karfi ja yaji, duk kuwa da umarnin kotu wanda ya dakatar da shi daga yin hakan.
A cikin sanarwar kungiyar ta kuma kai ziyara kwalejin noma ta Mando wadda ke karkashin jami’ar, wanda nan ne suke koken cewa gwamnan na shirin kwacewa.