Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta yi barazana sake fadawa sabon yajin aiki idan ta kammala taron majalisar Zartaswar ta nan gaba kadan.
Kungiyar ta ce wannan barazana ta yi ne don fargar da gwamnati ganin cewa har yanzu akwai mambobin ta da suke bin bashin albashi har na wata goma sha shida.
Ta ce baya ga kin biyan ƴaƴan ta albashin ma, akwai wasu kuma da ake zabtare musu wani kaso daga albashin nasu wanda kuma ta ce har yanzu babu wani abu da aka yi a kai.
Ta ce muddin gwamnati na son kada Ƙungiyar ta shiga wannan yajin aiki, to tilas ne a zauna teburin sulhu don samo bakin zaren wannan matsala.