By Ishaq Dabai
Kungiyar Tarayyar Afirka tace zata tsawaita da fadada ayyukanta na soji kan masu kishin Islama dake da alaka da Al-Qa’ida a Somaliya don shigar da wasu kasashe mambobin kungiyar, yayin da wa’adin aikinta na yanzu ya kusa karewa a ranar 31 ga watan Disamba.
Kasar dake yankin kahon Afirka ta fuskanci sabon rashin zaman lafiya a cikin ‘yan watannin nan, tare da jinkirta zaben da aka dade ana fama da shi da kuma takaddamar dake gudana tsakanin shugabanta da Fira Minista wanda ya janye hankali daga tashin hankalin da mayakan jihadi na Al-Shabaab suka yi.
Duk da korar mayakan daga Mogadishu shekaru goma da suka gabata, gwamnatin Somalia tana iko da wani yanki ne kawai na kasar, tare da muhimmin taimakon wasu sojoji 20,000 daga rundunar hadin gwiwa ta Tarayyar Afirka a Somalia (AMISOM).
AMISOM a yammacin Lahadin data gabata ta ce Kwamitin Sulhu da Tsaro na Kungiyar AU ya amince da matsawa zuwa wani aiki na hadin gwiwa tare da Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bada damar “sauran Kasashe masu sha’awar” shiga AU cikin ayyukan da ake yi da masu kishin Islama.
Shirin na bukatar amincewar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin birnin Mogadishu.
Sanarwar ta kuma bukaci Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmaajo, da Fira Minista Mohamed Hussein Roble dasu warware sabanin dake tsakaninsu tare da “sake mai da hankali kan kammala zaben da aka jinkirta ba tare da wani bata lokaci ba”.
Sanarwar tace “Rikicin siyasa dake gudana tsakanin Ofishin Shugaban kasa dana Fira Minista yana bada gudummawa ga tabarbarewar yanayin tsaro, yayin da hukumomin siyasa ke ganin hankalinsu ya shagala daga al’amuran gudanar da mulki,” in ji sanarwar.