By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, ta yi watsi da matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka na cire Najeriya daga jerin sunayen kasashe masu keta ‘yan cin addini a shekarar 2021, inda ta nemi alkaluman kididdiga da aka yi amfani dasu wajen isa ga matakin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ranar Juma’a ne gwamnatin Amurka ta cire Najeriya daga jerin sunayen ‘kasashen da suka damu musamman kan batun ‘yancin yin addini.
A cikin yin haka, gwamnatin Shugaba Joe Biden ta yi watsi da shawarar Hukumar Amurka kan ‘Yancin Addini ta Duniya, USCIRF.
Ficewar Najeriya daga cikin jerin sunayen na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka, Mista Antony Blinken ya fitar. Sanarwar ta zo ne kwana daya kafin zuwan Blinken Najeriya domin rangadinsa daya ke yi a Afirka.A cewar Blinken, ƙalubalen ’yancin addini a duniya a yau “tsari ne, kuma suna da ƙarfi sosai. Suna nan a kowace kasa.”
Kungiyar ta CAN, a cikin wata sanarwa, jiya data fitar, ta bakin shugabanta na kasa, Dr. Samson Ayokunle, tace har yanzu Kiristoci a Najeriya na fuskantar cin zarafi daga ISWAP, Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci.
Ayokunle yace kungiyar ta yi asara kan bayanai ko kididdiga da gwamnatin Amurka ta yi amfani dasu wajen ganin ta cire Najeriya daga cikin jerin sunayen.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnatin Amurka bata tuntube mu ba a lokacin da suka sanya Najeriya cikin jerin kasashen da suka shafi ‘yancin addini, haka nan ba su nemi ra’ayinmu ba kafin cire Najeriya daga cikin jerin sunayen. Idan da sun yi, da za mu iya kwatanta kididdigan da aka yi a wancan lokaci da kuma yanzu kan batun ‘yancin addini a Nijeriya.