Kungiyar Crystal Palace ta dauki Vieira a matsayin sabon mai horas da Yan wasa
Crystal Palace sun sanar da daukan Patrick Vieira babban dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, a matsayin mai horas da Yan wasan ta.
Vieira mai shekaru arba’in da biyar, wanda ya ja ragamar Arsenal lokacin da yake wasa, ya rattaba hannu zuwa shekara uku a kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace.
KARANTA:-Shekaruna sunfi karfin tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023: in ji el-Rufa’i
Vieira na daya daga cikin zakakuran Yan wasa a zamanin sa, in da ya baiwa Arsenal gudummawa sosai a tsakani 1997 zuwa 2005 a karkashin mai horas da Yan wasa Arsene Wenger. Yayi nasarar cin kofin premier biyu da kofin F.A guda hudu.
Bayan ya bar Arsenal ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus in da yayi kakar wasa daya sannan ya tafi Inter Milan, a inda ya samu nasarori da dama.
A fannin Kasa kuma, Vieira ya bugawa Kasar Faransa wasa har sau dari, cikin shekara 12, in da ya sami nasar cin kofin duniya a 1998, sannan yaci kofin nahiyar turai a 2000.