Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar daliban Najeriya ta kasa NANS a halin da ake ciki ta bayyana matsayinta kan bukatar da ministar ya yi na a gurfanar da ASUU a gaban kuliya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Sunday Asefon, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Ta Garkame Wasu Kamfanonin Takin Zamani Na Bogi 4
Asefon na mayar da martani ne kan kalaman ministan ilimi na cewa daliban da abin ya shafa su kai karar ASUU kotu domin neman diyya da aka yi a lokacin yajin aikin.
Da yake mayar da martani, Shugaban NANS ya ce ba za ta iya kai karar ASUU ba, yana mai cewa kungiyar ba ta mallaki ko kuma cin gajiyar kudaden da ake biya ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Watakila kawai abin da Malam Adamu Adamu ya samu tun da ya zama minista shi ne yadda daliban Najeriya ke bukatar a biya su diyya kan almubazzaranci da suka yi.
‘’Duk da haka, ministan yana da wayo da rabi ta hanyar ba da shawarar cewa ASUU ta dauki nauyin biyan bashin ba shine mai kula da manyan makarantunmu ba kuma ba shine mai cin gajiyar makudan kudaden da muke biya a manyan makarantunmu na Najeriya ba.’’
Indan dai za’a iya tunawa Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito ministan ilimi Malam Adamu Adamu yana cewa ya kamata ASUU ta dauki nauyin biyan daliban jami’o’in diyya na lokacin da aka bata musu, ba gwamnatin tarayya ba.
A wani labarin kuma, kungiyar Royal Commonwealth Society reshen Najeriya, ta yi alkawarin shiga tsakanin malaman da ke yajin aiki da gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da kayan aikin ‘diflomasiyyar ilimi.
Daraktan kungiyar na kasa, Mista Blackson Bayewumi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Abuja ranar Alhamis.
Bayewumi ya yi kira ga ASUU da ta rungumi tattaunawa mai ma’ana, tuntuba da sasantawa wajen warware yajin aikin da aka dade ana yi.