Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa-IPMAN ta dakatar da yajin aikin da take yi, tare da umartar mambobin ta dake matatar man fetur ta Enugu dasu dawo bakin aiki.
“A dalilin shiga tsakani da Manyan Hukumomi suka yi, sakamankon mummunan lamarin ylda ya faru a Sakatariyar mu, dake matatar mai ta Enugu, Kwamitin Zartaswa na Kasa na IPMAN ya janye aikin dake gudana a halin yanzu.
“Kamar yadda aka san yadda aiki yake da harkoki zasu dawo nan bada jimawa ba, a wuraren da lamarin ya rutsa da su a Enugu da Ebonyi da Anambara, wannan zai bada damar gudanar da tattaunawa yanda ya kamata, inji Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur na Kasa Alhaji Sanusi Fari, a cikin wani jawabi daya fitar a ranar Asabar, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kofin Aisha Buhari Na 2021: Afrika Ta Kudu Ta Yi Kaca-kaca Da Ghana
Idan dai ba’a manta ba, Shuwagabancin Kungiyar IPMAN a ranar Alhamis data gabata, ya umarci a daina ayyuka a matatar man fetur ta Enugu daga ranar Juma’a.
Shuwagabancin Kungiyar ya alakanta bada umarnin shiga yajin aiki, da hari da aka kai a Sakatariyar Kungiyar ta Enugu a ranar Alhamis, Wanda Jami’an Rundunar Yansanda suka kaddamar.
Kungiyar Dillalan Man Fetur Sai ta bada umarnin daina daukar man fetur a Enugu da Ebonyi da Anambara, lamarin da ya janyo hauhawar farashin man fetur a Jahohin.
Fari ya bayyana cewa, Shuwagabancin Kungiyar IPMAN ya sake dubi akan lamarin, tare da umartar mambobin ta dasu dawo gudanar da ayyuka da harkokin su.
Kamfanin Dillalan Labaru na Kasa ya ruwaito cewa, ya zuwa ranar Juma’a, ana sayar da litar man fetur a farashi na Naira 250 a gidajen mai, a yayinda a wajen hanya ana sayar da ita Naira Dari 500 a Jahohin da lamarin ya shafa.
A halin yanzu, farashin man fetur ya ya sauko Kuma ana Sai dashi akan Naira 165 kamar yadda doka ta sanya, biyo bayan janyewar yajin aikin.