Yayin da ake ci gaba samun ci gaba a lamuran yanar gizo a duniya, ƙungiyar Tarayyar Turai EU da kuma kasar Birtaniya zargin kasar Sin wato China da kutse a kafar Intanet.
Wannan kutse kamar yadda suka yi zargi, ya fi shafar kamfanin Microsoft ne da kuma masu amfani da manhajar kamfanin.
Tarayyar Turai EU ita ta fara fitar da sanarwar wannan zargi, yayin da ta ce manyan masana yanar gizo na kasar China sune ke da alhakin wannan aika-aika wanda tushensa shine babban birnin kasar.
Har wa yau ana sa ran kasar Amurka na gabda shigar da ƙara kan kasar ta China.
Kazalika kasashen sun dora alhakin wasu aika-aika ga intanet na kasashen duniya kan hukumar tsaron kasar China.
Masana binciken sirri na kasashen yamma sun ce wannan al’amari da China ke yi ka iya haifar da matsaloli muddin ba a taka mata burki ba.
Kawo yanzu dai ƙasar ta China ba ta ce ƙala ba game da wannan zargi.