By Abbas Yakubu Yaura
A ci gaba da kokarin ganin matan Fulani a jihar Nasarawa basu shiga cikin kowane irin aikata laifi ba, domin su zama masu dogaro da kansu, kungiyar raya al’adu ta Fulbe ta horar da mata kimanin 118 sana’o’i daban-daban.
Shugaban riko na kungiyar na jihar, Halilu Yahaya ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi a garin Keffi bayan horon daya dauki tsawon watanni hudu ana yinsa.
Ya bayyana cewa kungiyar ta fito da tsarin ne na horar da mata sana’o’i daban-daban domin su samu kwanciyar hankali, inda ya bayyana rashin aikin yi a matsayin babban abin dake kawo rashin tsaro a kasar nan.
Yahaya yace, “Dalilin daya sa aka samar da wannan shirin shi ne don a tabbatar da cewa matan Fulani guda 118 da aka zabo daga kananan hukumomin 13 na jihar suna da sana’o’in da zasu taimaka wajen sanya abinci a teburinsu, kuma na yi imanin cewa idan suna da wani abunyi rashin aikata laifuka zai ragu, domin rashin aikin yi shine babban dalilin da yake haifar da rashin tsaro a Najeriya.
Kazalika yace yana da matukar mahimmanci a taimaka musu, su sami ƙwarewa don kada su ɗauki laifi a matsayin zaɓi na rayuwarsu ta yau da kullun.sannan Mun fara gudanar da horon ne tun a watan Yuli kuma a yau za a basu kudi Naira 5,000 a matsayin alawus alawus din sufuri, daga nan kuma za a ba su jari don fara sana’o’insu.”
Shugaban gudanarwa na horar da kungiyar Hadiza Hussaini tace galibin matan da FUDECO ta horas dasu, basu da aikin yi domin basu da ilimi kuma basu da wata sana’ar da zata taimaka musu wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, shi yasa kungiyar ta kawo musu dauki.
Hadiza tace, “Mun horar da matan Fulani ne saboda mun lura cewa suna fuskantar kalubale da dama.Yawancinsu basu da aikin yi sannan kuma basu da ilimi kuma basu da wata sana’a. Wasu daga cikin matan sun kasance zawarawa kuma sun sha wahala shi yasa muka fito da shirin.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito “kungiyar zata basu karfin gwiwa da jarin fara kasuwanci domin su kasance masu dogaro da kansu da kuma ba da gudummawa mai ma’ana ga al’umma.”sannan Wadanda suka ci gajiyar tallafin da aka zabo daga kananan hukumomi 13 na jihar an koya musu yadda ake hada jakunkuna, takalma, waina, sabulu da dai sauransu.