Wakilinmu Mohammed Gambo Damaturu
Kungiyoyin fulanin Nahiyar Afrika dake karkashin hadakar Fulani mai rajin wanzar da zaman lafiya da kawo cigaba a Nahiyar wacce ake kira (AFPAD), ta yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano kan shirin sa na kirkiro da matsugunen makiyaya a jihar wanda ke tare da niyar kawo karshen matsalolin da suke fuskanta da kuma bunkasa walwalar su.
Wata wasika da aka turo ta adireshin e-mail din Gwamnan a jiya Juma’a 19 ga watan Yuli 2019 mai lamba:- AFR/FUL/III/19000/Z, wato kwana daya kenan bayan Ganduje ya kaddamar da kwamitin RUGA, Kungiyar ta yaba da abin da gwamnan yake yunkurin yi wanda ya jima yana kawo matsalar tsaro da tattalin arzikin kasar.
Wasikar dake dauke da sa hannun Ardo Cisse Malomea, wanda shine Shugaban hadakar kugiyoyin, ta ce kaddamar da kwamitin RUGA da Ganduje yayi, ya nuna cewa yana da kishin Nijeriya.
Kuma Yace wannan yunkurin ya karawa Fulanin Nijeriya da ma Nahiyar Afrika baki daya kwarin gwiwar samun cikakken gata daga Gwamnatin jihar Kano.
Wasikar tace “jihar Kano ta na sahun farko a jihohin Nijeriya a yunkurin inganta rayuwar talaka ba tare da nuna ban-bancin kabila ko matsayin al’umma ba, dan haka ya cancanci a yaba masa bisa la’akari da kasancewar sa shugaba abin kwatance a fannin kyautatawa jama’ar sa”.
A cewar wasikar, yadda Ganduje yayi na sauya yanayin kiwo daga daukar sa a matsayin gado zuwa hanyar bunkasa tattalin arziki abu ne da ya kyautu a yaba masa wanda kuma ya dace sauran Gwamnatocin kasar nan suyi koyi da shi musamman ma a yankin arewacin Nijeriya.
Wannan kungiyar tayi amanna da yunkurin gwamnatin jihar Kano wanda a ganin mu zai kawo sauyi mai kyau ga masana’antar matan Fulani na saida madara daga na da zuwa na zamani, inji wasikar.
Idan za’a iya tunawa dai, a ayyukan da aka baiwa kwamitin RUGA mai mambobi 16 akwai duba wuraren da sukafi dacewa da a gina rugagen makiyayan a cikin dazukan Jihar Kano.
“Mun kuma lura cewa matan Fulani dake sana’ar saida madara da basa yin ta a zamanace suma za’a inganta musu ita ta hanyar shigo da su kan sabuwar hanyar Zamani.
Kazalika wasikar ta jinjinawa Ganduje akan la’akari da yayi da dukkan bangarorin da abin ya shafa a cikin shirin, Wannan ma kadai zai bunkasa sana’ar su, inji wasikar.
Kungiyar ta cigaba da cewa ta ji dadin ganin yadda Ganduje ya lissafo ire-iren makiyayan da ake da su a Kasar nan wanda hakan zai sa a fahimci shirin sosai.
A lokacin kaddamar da kwamitin, Ganduje ya ce makiyaya kala uku ne, wanda suka hada da zaunannu, masu yawo daga arewa zuwa kudancin Nijeriya lokacin damina, da kuma masu shigowa da kasashen ketare.
Wasikar har wa yau ta kirayi gwamnatoci harma da gwamnatin tarayya da su kwaikwayi gwamnatin Jihar Kano.