Wata Kungiyar Fulani dake da zama a birnin tarayya Abuja da ta yi wannan kazalika ta bukaci sa a chafke Dan Rajin Raba Kasar Yarbawa Sunday Igboho da sauran masu hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikicin da ta kai ga an sauya wa Sarkin Fulanin Matsuguni tare da yin tabargaza wa dukiyoyin al’ummar Fulani.
Bisa ga haka, Ƙungiyar ta bukaci da biya Sarkin Fulanin diyyar dukiyar shi da aka lalata da ta kai ta Kusan Miliyan dari biyar sakamakon wutar rikicin.
Wadannan bukatu sun fito ne cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Ƙungiyar ta Kasa Alhaji Suleiman Yakubu da Sakataren sa Ibrahim Abdullahi bayan wata ziyarar nuna mubaya’a ga shugaban Fulani na Jihar Kwara.