Gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar jam’iyya mai mulkin Kasa ta (APC) sun amince su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin tattauna yadda za a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa da ke tafe.
Gwamnonin karkashin kungiyar gwamnonin jam’iyyar (PGF) sun cimma wannan matsaya ne a karshen taron da suka yi a daren ranar Lahadi a Abuja.
Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar PGF ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron da aka yi a rufe yasu isu.
Bagudu, ya ce bai san lokacin da za a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa ba. Amma “Mun amince a matsayinmu na kungiyar muna neman ganawa da shugaba Buhari don kuma tattauna babban taron jam’iyyar na kasa mai zuwa.
“Ku sani, mu bangare daya ne na jam’iyyar, kuma tun da muna ba da shawarwari ga jam’iyyar da shugabanninmu, ina ganin bai dace a yi gaba sasakai ba kafin a yi taron.
“Muna neman nadin da wuri-wuri, watakila nan da ‘yan kwanaki masu zuwa,” in ji shugaban PGF.
Bagudu ya ce kungiyar za ta sanar da jama’a game da matakin da ta dauka na raba ofisoshin zabe bayan ganawar ta da shugaba Buhari.
Sai dai ya ce zage-zagen da wasu ke yi na cewa gwamnonin na shirin ganawa da Buhari ne don su hana shi amincewa da kudurin dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima. “Wannan ba gaskiya ba ne. Ni dai na gaya muku abun da zamu gana da shugaban kasa shi ne don tattaunawa kan babban taron jam’iyyar na kasa mai zuwa,” inji shi.
Bagudu ya ce, taron ya kuma tattauna batutuwan da suka shafi shugabanci nagari, cigaban harkokin siyasa da sauran batutuwan da suka shafi cigaban jam’iyyar da kasa baki daya.
Ya ce taron ya zartas da kuri’ar amincewa da kwamitin riko na jam’iyyar karkashin Gwamna Mai Mala Buni da kwamitin tsare-tsare na musamman na jam’iyyar.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito Bagudu na cewa “Mun amince da kwamitin riko wanda ya yi aiki mai ban mamaki, wanda Gwamna Buni na Yobe da wasu gwamnoni biyu da ke cikin kwamitin ke jagoranta,” in ji shi.