Kungiyar Gwamnonin Arewa, ta bayyana kaduwar ta, da samun labarin rasuwar tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kaduna Architect Barnabas Yusuf Bala, Wanda aka fi sani da Bantex
Shugaban kungiyar Kuma gwamnan jihar Filato Barista Simon Bako Along ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, ta hannun Daractan yada labaran sa Dakta Makut Simon Macham, inda ya ce, Muna jimamin rashin Bala, tare da iyalan shi, Gwamnan jihar, da kuma al’umar jihar baki daya, bisa wannan babban rashi.
Lalong ya bayyana Marigayi Tsohon Maitaimaka Gwamnan, a matsayin Kwarare a fannin Zane-zane, Masanin Siyasa, Mutum Mai girma da Kima, Wanda ya yi aiki tukuru ga yankin shi, jihar Kaduna, dama kasa baki daya, bisa nuna jajirce wa, gaskiya da kuma kishin kasa.
Ya kara da cewa ” Dan uwan mu kuma abokin mu, Mutum ne da ya fi mai da hankali wurin tabbatar da aldalci, samun zaman lafiya, da kuma tabbatar da samun dai-dai-to ga addinai mabanban ta, tare da tabbatar da girma-ma kabilu, domin samun dauwa-mammen zaman lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya kamata mmyan fim murika auren junan mu~ Zakiyya
Kazalika ya kasan ce abun kwatance bisa yadda ya gudanar da aiyukan shi, a matsayin Babban Sakataran Kungiyar hadin kan al’umar Kudancin Kaduna wato SOKAPU, Ciyaman na karamar hukumar Kaura, Dan majalissa Mai wakiltar Karamar hukumar Kaura a majalissar dokokin kasar nan, Mataimakin Gwamnan jihar Kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2019, da kuma sauran mukaman da ya rike a tsahon rayuwar shi.
Along ya kuma ce, bayan kishin da BANTEX ke da shi wurin cigaban kasar nan, ya kasan ce Mai son ganin hadin kan yankin Arewa, domin magance matsalar Tsaro, Talauci, Cututtuka, Rashin Ilimi, da kuma magance Matsalar rashin fahimtar juna a tsakanin addinai ma banbanta.
A karshe ya yi wa Marigayin fatan samun Rahamar Ubangiji, da kuma bai wa iyalan sa hakuri rashin da aka yi, kana Gwamnan Lalong ya ce, Bartabar Bala Bantex, zata dade a na tunawa da ita.
Comments 1