Kungiyar Gwamnonin Arewa ta ce rasuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin CBN, Dakta Obadiah Mailafiya, babban rashi ne ga al’umma.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos a ranar Litinin ta hannun Daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Dr Makut Macham inda ya ce mutuwar Mailafiya abin bakin ciki ne.
Lalong ya ce rasuwar Mailafiya rashi ne ba ga iyalansa da mutanen jihar Kaduna kawai ba, rashi ne ga al’umma saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce marigayin kwararre ne a kan harkar kudi kuma haziƙi ne wanda aka san mutuncinsa a cikin gida da waje.
Gwamnan ya lurantar da cewa ilimin Mailafiya ya sanya gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu a duniya suka tafi da shi domin amfana da shi.
Shugaban ya jajantawa iyalan mamacin tare da rokon su da su kwantar da hankali ta hanyar duba abubuwan da ya wanzar, yana mai cewa yana da son ci gaba, ‘yanci, gaskiya, adalci da daidaito a dukkan ayyukan da ya yi a dandamali daban -daban.
Ya lura cewa hangen nesan sa na inganta Najeriya da ɗimbin waɗanda aka raunana ya sa ya yi takarar kujerar Shugaban Ƙasa a 2019.
Gwamna Lalong ya jajantawa Gwamna Nasir El-Rufai, gwamnati da al’ummar jihar Kaduna kan rashin Mailafiya tare da yi masa addu’ar Allah ya jikan sa da rahama.