Jam’iyyar PDP ta zabi gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin jamiyyar na kasa.
Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri ne ya sanar da hakan a karshen wani taron sirri da gwamnonin suka gudanar a ofishin gwamnan jihar Bauchi a ranar Asabar.
KU KARANTA: Cire Tallafin Fetur: Kungiyar NUJ Zata Tsunduma Yajin Aiki
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa gwamnonin jam’iyyar PDP, da yan kwamitin gudanarwarta na kasa, da masu ruwa da tsaki sun hallara a dakin taro na Banquet da ke fadar gwamnatin jihar Bauchi.
Nan da nan bayan an gudanar da bikin bude taron, sun shiga tarukan sirri na jiga-jigan jam’iyyar daban-daban.
Anan ne kuma suka iya tsayar da matsaya zabin da suka yi, bisa amincewar kowa a cikinsu.
Da yake sanar da hakan, Fintiri ya ce Mohammed ne ke maye gurbin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, inda ya kara da cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya zama Mataimakin Shugaban kungiyar.
Ya ce an zabi gwamnan jihar Bauchi ne bisa cancantarsa da kuma iya tafiyar da taron har zuwa wani matsayi.
A martaninsa, sabon shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da takwarorinsu domin ci gaban jam’iyyar.
Mohammed, wanda ya ce fitowar tasa ta zama abin alfahari a gare shi da daukacin al’ummar Jihar Bauchi, ya kuma bukaci takwarorinsa da su ba shi goyon baya don ciyar da kungiyar da kuma jam’iyyar PDP gaba.
A wani labarin kuma: Shugaba Tinubu Ya Jajantawa kasar Indiya kan Hadarin Jirgin Kasa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Indiya bisa wani mummunan hatsarin jirgin kasa.
Tinubu yace zuciyata na mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa a hatsarin jirgin kasa mai ban tausayi.
Hatsarin dai ya afku a ranar Juma’a baya ga wadanda suka mutu, wasu sama da 900 sun jikkata.