Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya bada umarnin haramta wani taro da Kungiyar Inyamurai take ƙoƙarin gudanarwa don Gudun kawo hargitsi da tun farko aka samu.
Taron wanda Kungiya Mai Suna Ƙungiyar Hadin Kan Al’ummar Inyamurai, an shirya gudanarwa ne a karamar hukumar Oyigbo a Ranar goma ga watan Afirelun da muke ciki.
A wata Sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa Paulinus Nsirim, gwamnatin ta umarci Jami’an tsaro fa su tabbatar da cewa wannan taro bai wakana ba, don ci gaba da wanzar da doka da oda a Yankin.
Ko da yake dai sanarwar bata zayyana takamaiman wani kalubalen tsaro ba ne take nufi, to amma karamar hukumar ta Oyigbo ta yi iyaka da Jihar Abia inda nan ne Ƙungiyar Inyamurai ta IPOB ta fi Karfi wanda aka ayyana ta a matsayin Ƙungiyar da ta kai wasu hare hare kan yan sanda da Kayyakin aikin su.
Kuma harin ya haifar da barin wuta daga jami’an soji, wanda ya kai ga an hallaka sojoji da Fararen hula.
Kazalika baya ga Zanga-zangar EndSARS da ta gudana a watan Oktoba a yankin na Inyamurai, taron kungiyar na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a ofishin yan sanda da kan al’umma a yankuna Inyamurai.