Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, tace matuƙar ba’a ɗauki matakin da ya dace akan Abdulmalik Muhammad Tanko da ake zargi da kashe Hanifah Abubakar ƴar shekara biyar bayan da yayi garkuwa da ita ba, to kuwa zasu shige gaba domin yin abinda ya dace.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na kungiyar Muhammad A-A King, ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke dasa hannunsa aka rabawa manema labarai a wannan rana ta Asabar.
Sanarwar ta ƙara da cewar, “Munsan dukkanin irin abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan na ƙarancin ɗaukar mataki akan al’amarin makamancin na Hanifa da ya faru, don haka muke kira da kakkausar murya da a ɗauki matakin da ya dace akan kisan Hanifa Abubakar ko kuma mu wuce gaba har muga an ɗauki matakin da ya dace,
domin kuwa aikata hakan zalunci ne da rashin imani tsantsa, inji A-A King.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ga dukkanin dai masu bibiyar kafafen yaɗa labarai dama wasu daga cikin shafukan sada zumunta, suna da labarin yin garkuwa da Hanifah kimanin tsawon kwanaki 47, wanda kuma da aka tsananta bincike aka gano cewar malamin makarantarsu ne mai suna Abdulmalik Muhammad Tanko ya kasheta bayan da yayi garkuwa da ita inda ya nemi bashi kuɗin fansa har naira mulyan 6.
Haka kuma, Shugaban Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin Ambasada Karibu Yahya Lawan Kabara yace, matuƙar jami’an tsaro da ma’aikan Shari’a harma da ɓangaren gwamnatin Kano ba su ɗauki matakin da ya dace ba, babu shakka zasu ɗauki matakin doka a duk ɓangaren da aka samu sakaci, tunda dai itama yarinyar da iyayenta suna da haƙƙi.
“Idan ma iyayenta sun yafe jininta mu bamu yafe ba zamu cigaba da bibiyar lamarin har sai munga haƙƙin Hanifa Abubakar ya fita, inji Ƙaribu Kabara, a cikin sanarwar