Kungiyar kare hakkin bil’Adam ta majalissar dinkin duniya a jiya talata ta ce, da yuwuwar ta shirya wani gaggami a wannan makon kan halin da kasar Sudan ke ciki sakamakon juvin mulkin da a kayi, a makon jiya.
Taron zai gudana ne da musalin karfe 11:30 agogon GMT a ranar juma’a mai zuwa, kamar yadda kungiyar kare hakkin bil-Adaman ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne bayyan wani Taron gaggawa da kasashe, Amurika, Norway, da kuma Jamus sukayi da wasu jerin kasashen duniya a ranar litinin din data gabat, kan halin da Kasar Sudan ke ciki bayan Juyin mulkin da Sojin kasar suka yi.
Idan za’aiya tunawa cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar nan ne, Janar Abdel Fattah AL-Burhan ya rusa majalissar zartarwar hadaka na kasar Sudan, wanda aka samar da ita, tun bayan hambarar da tsohon kasar Omar Al-Bahsir daga ofishin sa a shekarar 2019.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanayin da Ake Ciki Kan Kwararar Iskar Gas A Legas
Kazalika daga bisani Janar Burhan ya sanar da sanya dokar ta baci a kasar, tare da tsare wasu shuwagabannin fararan hula na kasar, da ya hadar da Faraminista Abdalla Hamdok da jami’an gwamnatinsa