By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi kira da a gaggauta daukar dokar kare hakkin yara mata domin hana yawaitar aurar da kananan yara, inda ta zargi kundin tsarin mulkin kasar da cin karo da dokar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata, kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta yi nuni da cewa, auren kananan yara ya zama ruwan dare a kasar kuma a cikin mafi girma a nahiyar, sakamakon rashin aiwatar da doka daga gwamnatocin tarayya da na jihohi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ko da yake dokar kare hakkin yara ta tarayya (CRA, ta shekarar 2003) ta haramta auren ‘yan mata ‘yan kasa da shekara 18, amma kundin tsarin mulkin Najeriya ya kunshi wasu tsare-tsare da suka yi hannun riga da wannan matsayi.
“Jahohin da ke da tsarin shari’ar Musulunci su ma sun kasa bin dokar tarayya da kuma ‘yan shekara 18 a matsayin shekarun da suka kai ga aure. Wasu jihohin Kudu da suka karbi wannan matsayi sun kasa daukar kwararan matakai don aiwatar da shi.”
A cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, kasancewar kasar da ta fi kowace kasa yawan al’umma a Afirka, Najeriya ce ta fi kowacce yawan aurar da ‘ya’ya mata kanana da aka yi kiyasin cewa akwai yara miliyan 22 da aka aurar da su kafin su balaga.
Da wannan adadin Najeriya ce ke da kashi 40 cikin 100 na adadin yaran da ake aurawa a Afirka inda kasar Nijar ke da kashi 76 cikin 100, wadda ita ce ta daya a duniya, sai Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai kashi 68 cikin 100, sai Chadi mai kashi 67 cikin 100.
A cikin sanarwar, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta gano cewa auren ‘ya’ya mata ya zama ruwan dare a jihohin Imo da Kano, duk da cewa tsohuwar dokar ta dauki CRA a shekarar 2004. A karshen dokar dai tana jiran amincewar gwamna ne bayan ta zama doka a watan Fabrairun shekarar data gabata 2021.
Daraktan Afirka a Human Rights Watch, Mausi Segun, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su gaggauta daidaita CRA da dokokin da ake da su don kare yancin ‘yan mata.
Jaridar Dimokuradiyya ta jiyo shi yana cewa, “Abin takaici ne yadda kusan shekaru ashirin da kafa dokar kare hakkin yara, har yanzu ana tilastawa ‘yan matan Najeriya auren wuri.
“Ya kamata jihohin Najeriya su gaggauta daukar matakin aiwatar da su, da kuma daidaita dokokin da ake da su da tanadin dokar kare hakkin yara, wanda ya haramta aure kafin su kai shekara 18 da kuma kare hakkin ‘ya’ya mata.”
Kungiyar ta kuma yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ci karo da kundin tsarin kare hakkin kananan yara na Afirka da kuma yarjejeniyar kare hakkin yara ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta sanya shekarun 18 a matsayin shekarun da ke ba wa yara ‘yanci daga tashin hankali da sauran batutuwa. .
Kazalika “Auren yara ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yan cin yara, wadda ta tabbatar da cewa shekarun haihuwa 18 ne, kuma ya ba wa yaro ‘yanci daga tilastawa da tashin hankali, da samun kula da lafiya da ilimi.
“Akwai bukatar Najeriya cikin gaggawa ta daidaita dokokinta don dacewa da ka’idojin dokokin kasa da kasa don kare yara daga aure,” Human Rights Watch ta gano cewa.
“Yakamata a amince da dokar kare hakkin yara kuma a aiwatar da ita a dukkan jihohi. Ya kamata gwamnatin tarayya da hukumomin jihohin da suka amince da dokar su samar da wani kwakkwaran tsarin aiki don tabbatar da aiwatar da doka yadda ya kamata da kuma sanya takunkumin karya doka,” in ji sanarwar.
Sannan “Ya kamata dukkan jihohin Najeriya su karfafa dokoki tare da samar da ingantattun tsare-tsare don tilasta su don tabbatar da walwala da lafiyar ‘yan matan Najeriya,” in ji ta.