Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Imo ta nemi afuwar cocin Anglican kan mamaye cocin da jami’an tsaro suka yi.
Shugaban kungiyar ta CAN a jihar, Reverend Eches Divine-Eches, ya mika takardar afuwar a madadin kungiyar a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake ganawa da manema labarai a Owerri, babban birnin jihar.
“Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Imo tana ba wa cocin Anglican hakuri kan lamarin da ya faru na kama Uche Nwosu a daya daga cikin majami’un ta. “Mun yi imanin cewa za a iya guje wa hakan.”
‘Yan sanda sun kai farmaki cocin St. Peter’s Anglican da ke Eziama-Obaire a karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya janyo cece-kuce a sassan kasar.
Jami’an tsaro dauke da muggan makamai sun afkawa cocin da manyan motocin tsaro inda suka yi ta harbe-harbe ta sama kafin su cafke Mista Uche Nwosu, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a Imo kuma sirikin tsohon Gwamna Rochas Okorocha.
Da yake yin Allah wadai da matakin da ‘yan sandan suka dauka, Divine-Eches ya bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar sun gudanar da aikinsu cikin kwarewa.
Ya bukace su da su guji ayyukan da za su iya ba masu cin zarafi da masu aikata laifuka damar lalata ayyukansu nagari.
Limamin, ya bayyana cewa kungiyar za ta cigaba da bayar da goyon baya ga duk wani yunkuri da jami’an tsaro za su yi na kame duk wata kungiya ko wani da ke da hannu a cikin kowane irin laifi a jihar.
“A matsayinmu na kungiyar Kiristocin jihar, muna goyon bayan kokarin da jami’an tsaro ke yi na ganin an gurfanar da duk wani mutum da aka samu da hannu a duk wani nau’i na aikata laifuka a jiharmu,” in ji shi.
“Dole ne jami’an tsaro su lura da yanayin aiki don gujewa bata hankalin jama’armu tare da ba masu zagi damar yin lalata da kyawawan ayyukansu ba tare da son rai ba.”