Shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya CAN a jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata sun sake jaddada kin amincewa da tsarin yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa addini daya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa jam’iyyar APC itace mai wannan tsari na Musulmai zallah a zaben 2023, Sun bayyana cewa ba za su sauya matsayarsu na adawa da tikitin takarar shugaban kasa na musulmi da musulmi ba.
Shuwagabannin sun bayyana matsayar su ne a wani taro da Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilai da Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya suka kira a Abuja.
KARANTA ANAN: An Samu Sabani Da Ministar Kudi Da Majalisar Dattawa Kan Kasafin Baɗi
Tsohon shugaban majalisar wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa taron da shugabannin kiristoci na Arewa da na babban birnin tarayya Abuja sunyi shi ne don tabbatar da matsayar su a 2023.
Dogara ya bayyana cewa ana ci gaba da fafutukar tabbatar da adalci, inda ya kara da cewa sun gudanar da taron tuntuba da shugabannin addinin Kirista na jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja kan tsarin da Najeriya ta dauka a shekarar 2023.
A wani labarin kuma: Cutar Ƙyanda Ta Kashe Mutane 190, An Samu Mutane 422 Da Jabun Katin COVID-19
Darakta-Janar na Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Ifedayo Adetifa, ya ce mutane 18,577 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kyanda da kuma mutuwar mutane 190 a cikin mako na 35 a jihohi 36 da babban birnin tarayya.
Ya bayyana hakan ne a Abuja jiya yayin taron ministoci da sabbin bayanai kan cutar COVID-19 da ci gaba da aka samu a bangaren kiwon lafiya.