Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta rubutawa dukkanin kungiyoyin ta 43 da suka hada kai domin tsunduma yajin aiki da aka tsara za a fara a ranar Laraba 7 ga watan Yuni, 2023, inji rahoton The PUNCH.
Yajin aikin ya biyo bayan karin farashin litar man fetur, da gwamnatin tarayya tayi.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Real Madrid Ta Soke Kwantiragin Eden Hazard
Wasu daga cikin kungiyoyin NLC sun hada da – Kungiyar Malaman Jami’o’i, Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Kasa, Kungiyar Malamai ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan jinya ta Kasa da Ungozoma da dai sauransu.
A cikin wata wasika da ta rubutawa kungiyoyin da ke dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja, kungiyar ta bukaci su akan su mara mata baya domin kawo karshen halin kunci a Najeriya.
Kungiyar dai ta yanke shawarar za ta fara wani mataki da janye ayyuka a fadin kasar, a kan yadda ake shiga wani wajen siyen litar man Fetur.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne, yayin jawabin bude taro a dandalin Eagle Square da ke Abuja, shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa zamanin biyan tallafin man fetur ya kare.
Tinubu ya kuma bayyana cewa kasafin kudin 2023 bai yi tanadin tallafin man fetur ba, don haka karin biyan kudin bai dace ba.
A wani labarin kuma: Kano: Kungiyar NULGE Ta Nemi Hadin Kan Gwamnan Kano Domin Aiki Tare
Kano: Kungiyar NULGE Ta Nemi Hadin Kan Gwamnan Kano Domin Aiki Tare