Kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci kungiyar ta jihohi da su shiryawa tafiya yajin aiki a ranar 16 ga watan Oktoban nan. Inda ta jaddada cewa musamman ma idan tattaunar da suke yi da gwamnatin tarayya dangane da yiwuwar biyan naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ya ci tura.
Babban Sakataren kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja shi ne ya tabbatar da hakan
a wata takarda da ya aikawa da shugabannin kungiyar na jihohi.
Ya kara da cewa; da zarar zaman da za su yi da gwamnati a ranar 15 ga watan Oktoba bai cimma nasara ba, a shirya tafiya yajin aiki kawai.