Hadaddiyar Kungiiyar Kwadago ta Jihar bauchi ta ce za ta tsunduma wani yajin aikin sai baba ta gani daga ranar talata 23 ga watan maris din shekarar da muke ciki.
Sungiyar ta tsaida wannan matsaya ce biyo bayan wani taron majalisar zantaswar ta da ta gudanar a Bauchi.
Shugaban kungiyar Kwamared Danjuma Saleh wanda ya bayyana cewa tsunduma wannan yajin aiki ga kungiyar ya zamo wajibi don ganin sun matsa kaimi ga gwamnati ta biya musu bukatun su.
Danjuma Saleh ya ce akwai bukatu da dama da kungiyar ke fama da su da suka hada da tsaiko wajen samun albashi a kan kari, matsalar fansho da giratuti, matsalar karin girima ga maaikata da kuma matsalar cire musu wani kaso daga albashi.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa kungiyar ba za ta zura idanu tana kallo abubuwa na ci gaba da tafiya sakaka ba, don haka ne kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta biya mata bukatun ta don gujewa fada wa yajin aikin.