Wani Farfesa Kan harkokin Shari’a a Jami’ar Ilori dake Jihar Kwara Ibrahim Abdulqadir Abikan ya ce lallai akwai abin dubawa dangane da yadda Masu Rajin Kare Hakkin Bil’adama da ma Kungiyoyi masu faɗa suka ja bakin su suka yi gum kan yadda ake ci gaba da samu rashin fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista a Jihar Kwara kan batun Sanya Hijabi.
Abikan wanda Shine Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi ta Kasa ya bayyana haka ne a yayin zantawar shi da Jaridar Daily Trust, inda ya ce dole ne Ƙungiyar Lauyoyi ta Kasa NBA da Babban Lauyan Nan Femi Falaba su fito su nuna matsayar doka wa al’umma kan Wannan al’amari.
“Abin bakin ciki ne da takaici a ce mutane irin su Femi Falana suna nan amma su ja bakin su su yi shiru ana ta cin zarafin mata musulmi a Jihar duk da irin hukunci da kotu ta yanke” Abikan.
“Haka Zalika su ma Kungiyoyi irin na Lauyoyi ta Kasa da ma mas kare hakkin Bil’adama da suke ikirarin wanzar da dokoki a ce sun ja bakin su sun yi gum, kamata ya yi a ce sun fito sun yi magana indai har da gaske suna kare hakkin farar hula ne”
Ya kara da cewa kawo yanzu dai Ƙungiyar MULAN ba ta tsaida matsaya ba kan wannan dambarwa, inda ya ce suna jira ne su ga matakin Ƙungiyar Lauyoyin gabannin bayyana tasu matsayar.
Kazalika Abikan Ya zargi Kungiyar Kiristoci ta CAN ta yunkurin rura wutar rikicin, inda ya bukace ta da ta kasance mai wanzar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristan Jihar kamar yadda aka sani tun tale-tale.
Da aka tuntube shi, Lauyan Ƙungiyar CAN da Kuma Makarantun Mishinari Barista Akin Akintoye ya ce kawo yanzu ba zai ce komai ba game da hakan ganin cewa har yanzu maganar tana gaban Kuliya.