Kungiyar ma’aikatan bangaren Shari’a a kasarnan ta janye yajin aikin da ta shiga kimanin wata biyu da ya gabata.
A yanzu haka wannan mataki na nuni da cewa ma’aikatan za su koma bakin aiki daga ranar Litinin makon gobe.
Kungiyar ta tsaida wannan matsaya ne yayin wani taron majalisar zartsawarta da ta gudanar yau talata a birnin tarayya Abuja.
Kawo yanzu dai babu wani yarjejeniya da Kungiyar ta fitar da ta yi silar janye wannan yajin aiki.