By Abbas Yakubu yaura
Kungiyar Malamai a babban birnin tarayya sun dakatar da yajin aikin da suka kwashe tsawon makonni biyu suna yi na masana’antu.
Kungiyar malamai ta Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar a ranar 18 ga watan Nuwamba kan rashin biyan su alawus alawus da sauran su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello. A wannan rana ya gana da shugaban NUT na babban birnin tarayya Abuja, Stephen Knabayi, inda ya yi alkawarin biyan duk wasu bashin da malaman suke bi kafin karshen shekara.
Sai dai malaman sun ci gaba da yajin aikin sai baba-ta-gani a karshen yajin aikin gargadin da suka yi na neman biyan bukatunsu bayan da shugabannin majalisar yankin suka ki jin ta bakinsu.
Da take zantawa da wakilinmu a ranar Laraba, Sakatariyar kungiyar reshen babban birnin tarayya Abuja, Margaret Jethro, tace an cimma matsayar kan dakatar da yajin aikin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar a ranar Talata.
Ta ce, “Mun yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan gudanar da wani taron gaggawa da majalisar zartaswar reshen babban birnin tarayya ta yi.
“Wannan ya biyo bayan kudurin shugabannin kananan hukumomin yankin na aiwatar da karin girma na shekarar 2019 da 2020 a cikin albashin watan Nuwamba.