Kungiyar Malaman Jami’o’i ta bayyana ranar Litinin 7 ga watan Fabrairu, 2022 a matsayin ranar da babu karatu domin wayar da kan dalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a kan rikicin da ya kunno kai sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla cikin adalci.
Wata sanarwa da shugaban kungiyar ASUU na Jami’ar Bayero Kano, Kwamared Haruna Musa da kuma Kwamared Yusuf U. Madugu suka sanyawa hannu a ranar Alhamis, ta ce matakin ya yi daidai da sakatariyar kungiyar na kasa domin fadakar da masu ruwa da tsaki halin da ake ciki a cibiyar ilimi.
ASUU ta yi iyakacin kokarinta kuma ta saurari muryoyin hikimar ‘yan Najeriya da dama masu son zaman lafiya da kungiyoyi na dakatar da yajin aikin na Disamba 2020 domin baiwa Gwamnatin Tarayyar Najeriya damar yin abin da ya dace don ceto tsarin Jami’o’in Najeriya daga ci gaba da tabarbarewar, ”in ji sanarwar.
‘’Amma duk da haka, FGN ta yi watsi da duk wata kyakkyawar fata da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka yi kan hanyar da za a bi wajen warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin ASUU da FGN.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa kungiyar ta amince da tsoma bakin da kungiyar hadin kan addinai ta Najeriya (NIREC) ta yi a baya-bayan nan don magance rikicin da ya dabaibaye kasar, tare da yin kira ga FGN da ta saurari kalaman hikima domin dakile wani cikas na kalandar ilimi a Jami’o’inmu.
‘’ASUU-BUK na son sanar da duk masu ruwa da tsaki cewa duk wani mataki da ASUU za ta dauka zai kasance da amfani ga tsarin Jami’o’in Najeriya. Don haka kungiyar ta bukaci masu hannu da shuni da su hada kai da ASUU domin ganin an ceto tsarin Jami’o’in Najeriya daga rugujewar da ke tafe ta hanyar yin galaba a kan Gwamnati wajen aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da ASUU cikin gaggawa.’’