By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kungiyar masu babur mai kafa uku na Kaduna ya nemi afuwar gwamnatin jihar Kaduna bisa karya dokar hana zirga zirgar babura da wasu mambobin kungiyar suka yi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Oktoba, shekarar 2021, gwamnatin jihar Kaduna ta fara aiwatar da dokar hana zirga zirgar babura da kuma hana babura yin aiki daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yamma.
Neman afuwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban KATOA, Aminu Ibrahim, a Kaduna.
Ibrahim ya kuma roki gwamnatin jihar da ta saki baburan masu kafa ukun da jami’an tsaro suka kama.
Ya ce, “Wannan neman afuwar ya samo asali ne a kan yadda mambobin kungiyar da suka hada da ma’aikata ke gudanar da sana’ar tuka babura masu kafa uku da nufin yin sana’ar da ta dace domin samun abin dogaro da kai.
“Haka zalika, akasarin binciken da muka gudanar ya nuna cewa, galibin wadanda suka karya dokar hana hawa babur mai kafa uku daga karfe shida na safe zuwa karfe 7 na yamma, ba su yi hakan da gangan ba.
“Sakamakon cunkoson ababen hawa ne a lokacin da yake tashin gwauron zabi inda akasarin mahaya ke kan hanyarsu ta zuwa ko dai su isa gidajensu ko wuraren ajiye motoci da kuma fasinjojin da ba su da zabin isa inda suke daban-daban musamman mata da tsofaffi.
“Muna roƙon ku da ku yi la’akari da buƙatarmu kuma ku ba mu dama ta biyu.”
Ibrahim ya ce kungiyar ta fara yakin neman zabe ta kafafen yada labarai tare da jajircewa da sauran wayar da kan jama’a da nufin fadakar da ’ya’yan kungiyar kan keta hakki.
“Muna tabbatar wa gwamnatin jihar cewa mambobin kungiyar za su bi ka’idojin da aka kayyade.
“Za mu ci gaba da ba da gudummawar kason mu wajen aiwatar da umarnin Gwamnatin Jiha,” in ji shi.