Daga Zahraddeen Sirajo Abbas
Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Biredi Ta Kasa, Alhaji Mansir Mansi ya bayyana cewa a duk fadin kasar babu wata kungiyar da ke baiwa matasan ayyukan yi a kasar idan aka fitar da hukumomi gwamnati.
Shugaban Kungiyar Alhaji Mansir Mansi, wanda kuma shi ke da sanannen gidan Biredin nan a Katsina ya bayyana haka ne lokacin wani taron karramawa da kungiyar ta shirya domin taya shi murnan samun wannan mukami na Shugaban masu Biredi na tarayya Nijeriya, a dakin taro na Service To Humanity, dake Gidan Dawa, a cikin garin Katsina.
Alhaji Mansir Umar ya ci gaba da cewa akwai gidan biredi anan cikin garin Katsina, yana da ma’aikata sama da dari, gidan biredi kowa zai iya zuwa ya nemi abinci ko ya yi karatu ko bai yi ba, Ina nufin karatun zamani ko bai yi ba, yana da gurbi a wajen mu. Sannan masu gidajen biredi suna ba matasan da ke aiki na su koma makaranta domin karo karatu, wato suna aiki kuma suna karatu.
Daga karshe ya yi godiya ga Membobin da irin hadin kai da suke bashi, kuma ya sha alwashin kawo wa kungiyar ci gaba mai dorewa da tabbacin ci gaba da jajircewa ganin duk tallafin da gwamnatin tarayya da ta jiha ke badawa ganin ‘yayan wannan kungiyar sun amfana.