Kungiyar Masu Kamfunan Harkar Sufuri Ta Kasa, NANTA ta karrama Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, a matsayin gwamnan da yayi fice kan samar da yanayi mai kyau ga harkokin yawon shakatawa da manyan ayyukan raya kasa domin jin dadin al’ummar jihar.
Bikin karramawar ya gudana ne a dakin taron na cibiyar taruka ta ƙasa da ƙasa da ke babban birnin tarayyar Abuja.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero shine ya mikawa Mai Girma Gwamnan lambar yabon a madadin shugabannin kungiyar.
Gwamnan kuma ya sami rakiyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kano, Hon. Zubairu Hamza Massu; Kwamishinan yada labarai, Comrade Muhammad Garba; Kwamishinan Al’adu Da yawon bude Idanu, Hon. Ibrahim Ahmad Karaye; Shugabar matan Jam’iyyar APC, Hajiya Fatima Dala; Ma’ajin Jam’iyyar APC, Hajiya Yardada Mai Kano; Mai baiwa Gwamna shawara a kan Harkokin Ma’adinai, Hajiya Balaraba Kapag; Mai Baiwa Gwamna shawara a kan Harkokin lafiya, Dr. Fauziyya Buba da Sauran Jami’an lafiya.